Wani jami'i a yankin ya ce akwai mutane da dama da ake kyautata zaton sun makale a baraguzan gidajen da suka ruguje.
Girgizar kasar data kai maki 6 da digo 4 ta abkawa yankin dake gabar teku ne da sanyin safiya.
Wasu hotunan talbijin sun nuna masallatai da gidaje da wasu wuraren sun yi kaca-kaca a garin Pidie Jaya.
A shekarar 2004 al'ummar lardin Aceh sun fuskanci mummunar girgizar kasa da guguwar tsunami ta haddasa data kwashe wasu kauyukan dake gabar tekun India.288